'Yan takarar gwamna da 'yan majalisa sun kai 6,000

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane za su shafe lokaci mai tsawo a kan layi

Hukumar zaben Nigeria- INEC ta ce mutane 6,050 ne ke yin takarar kujerun gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a zaben da za a yi ranar Asabar.

A wata sanarwa da kakakin hukumar zaben, Mr Nick Dazang ya aike wa manema labarai, ya ce a cikin su, mutane 760 ke yin takarar kujerun gwamnoni, yayin da mutane 5,290 ke yin takarar kujerun 'yan majalisar dokokin jihohi.

Ya kara da cewa za a yi zaben ne a jihohi 29 cikin 36 na kasar.

A cewarsa, jihohin su ne: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Bauchi da Benue da Borno da Cross River da Delta da Ebonyi da Enugu da Gombe da Imo da Jigawa da Kaduna da kuma Kano.

Sauran su ne:Katsina da Kebbi da Kwara da Kogi da Lagos da Nasarawa da Niger da Ogun da Osun da Oyo da Plateau da Rivers da Sokoto da kuma Zamfara.

Mr Nick ya ce jihohin da ba za a yi zaben gwamnoninsu ba su ne: Anambra da Bayelsa da Edo da Ondo da Osun da Ekiti da Kogi da kuma babban birnin Tarayyar, Abuja.

Hukumar zabe ta ce ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin ganin an yi zabe a jihohin ba tare da matsala ba.