Buhari ya yabi hukumar INEC

Shugaban Nigeria mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi a galibin sassan kasar.

A wata hirarsa da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai a garin Daura, mahaifarsa, Janar Buhari ya ce duk da cewa an samu barkewar tashe-tashen hankula da kuma satar akwatunan zabe a wasu sassa na kasar, amma hukumar zabe mai zaman kanta ta yi kokari kwarai da gaske.

" A wannan karon 'yan matsalolin da aka samu a baya an magance su idan aka kwatanta da abubuwan da suka faru a zaben shugaban kasa. Ni a gani na hukumar zabe ta yi kokari," in ji Janar Buhari.

Ya kara da cewar "Rikicin da aka yi a yau, bai kai na zaben shugaban kasa ba, sannan mutane basu fito yin zabe sosai ba."

Janar Buhari a makonni da suka wuce ne ya samu nasara a zaben shugaban kasa inda ya samu galaba a kan Shugaba Goodluck Jonathan.