Masar: An yanke wa Badie hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An aiwatar da hukuncin kisa kan Muhammad Badie a Masar

Wata kotu a kasar Masar ta tabbatar da aiwatar da hukuncin kisa kan Mohammed Badie, jagoran kungiyar 'yanuwa Musulmi ta ''Muslim Brotherhood'', da wasu mambobin kungiyar wacce yanzu aka haramta.

An same su da aikata laifin kitsa rudani da tashin hankali a kasar.

Shima wani ba Amurke dan asalin kasar ta Masar Mohamed Soltan, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan marawa kungiyar ta ''Muslim Brotherhood'' baya, da kuma yada labaran karya.

Daruruwan 'yan kungiyar ne aka yanke wa hukunci daga na kisa zuwa na daurin rai-da-rai, tun bayan hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi a shekara ta 2013.

Alkalin kotun Mohamed Nagy Shehata ne ya karanta sunayen wadanda aka yankewa hukuncin.

Ya ce '' Duka membobin wannan kotu sun amince ba tare da wata-wata ba, kan hukuncin da aka yankewa wadannan mutane--ciki har da Mohammed Badie, an kuma yanke musu hukuncin kisa kan duk abinda suka aikata."