Yau a ke zaben gwamnoni a Najeriya

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Masu kada kuri'a a Najeriya

A yau ne 'yan Najeriya ke fita domin zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi.

Hukumar zaben kasar ta ce ta kammala dukkanin shirye shiryen gudanar da zabukan ba tare da an ci karo da matsaloli ba.

Hukumar ta ce ta koyi darussa daga zaben shugaban kasar daya gudana ranar 28 ga watan Maris, inda a ka ci karo da matsalar rashin kai kayan zabe runfunan zabe a kan lokaci da kuma gaddamar da na'urar tantance masu kada kuri'a tayi a wasu wurare.

Mista Nick Dazang, mai magana da yawun hukumar zaben Nigeriyar ya ce hukumar ta dauki matakan kaucewa matsalolin da aka fuskanta a zaben shugaban kasar.

"Mun dauki matakin kaucewa makara wajen isar jami'an zabe rumfunan zabe, kuma wajibi ne ayi amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a a duk kan jihohin da zaben zai gudana" inji Mista Dazang.

Hukumar zaben ta ce daga karfe 8 na safe ne za'a tantance masu kada kuri'a sannan a fara kada kuri'a daga karfe daya da rabi na rana.

Jihohin da ba za a gudanar da zaben gwamnoni ba a yau sun hada da Anambra da Bayelsa da Edo da Ekiti da Kogi da Ondo da Osun da babban Birnin Tarayya Abuja.