Kai tsaye: Zaben gwamnoni da 'yan majalisa

Latsa nan domin sabunta shafin.

Hakkin mallakar hoto Abdulrazaq Yusuf

Barkanmu da warhaka da kuma ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan zaben Najeriya na 2015. A yau ne 'yan kasar ke sake komawa rumfunan zabe domin zaben Gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohin kasar, bayan da a karshen watan jiya suka zabi shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin tarayya.

  • A jihohi 29 za a gudanar da zaben gwamnoni a yayinda a jihohi 36 za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki na jihohi.
  • Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

15:56 Wakilinmu Annur Muhammad Annur a jihar Jigawa ya shaida mana cewa 'yan sanda sun harbi wani mutum mai suna Baba Audu sakamakon satar akwatin zabe da yaje yi a mazabar Unguwar Yayari da ke garin Hadeja a jihar Jigawa.

Hakkin mallakar hoto BBC Hausa WhatsApp
Image caption Masu kada kuri'a a fadar gabas da ke Gwaram a jihar Jigawa, inda akwai kananan yara masu kada kuri'a

15:44 A jihar Adamawa kuma, rahotannin da muke samu yanzu na cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar da janye dokar hana fita daga gobe Lahadi zuwa ranar Talata wadda tun farko ta bayyana kafawa.

15:43 Wakilinmu a Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce an samu rahotannin yin awon gaba da akwatunan zabe a wasu mazabu guda uku a jihar ta Lagos.

15:41 A jihar Lagos, babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya rahotanni na cewar ana gudanar da zaben cikin lumana, ko da yake babu yawan jama'a a mazabu da dama.

Image caption Mutane sun ci gaba da kasuwancinsu a jihar Bauchi a lokacin da ake zabe

15:37 Kakakin hukumar INEC, Mr Nick Dazan ya bayyana cewa an harbi wani shugaban jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi, inda kuma nan take ya rasa ransa.

15:35 Anas Saminu Ja'en daga Kano, ya aiko mana sako ta shafinmu na sada zumunta inda ya ce, "Yanzu haka misalin karfe 2:00 na rana a mazabata da ke Ja'en a karamar hukumar Gwale a Kano a akwatina da sauran akwatuna mun kammala zabe lafiya yanzu haka muna zaune munyi cirko-cirko muna jira zuwa anjima a fara kirga sakamako."

Image caption An baza jami'an tsaro a Kaduna da kewaye domin kaucewa tabarbarewar tsaro.

15:24 Wakilinmu, Ishaq Khalid ya ce hatsaniyar ta kaure ne sakamakon zargin da wasu suka yi na cewa magoya bayan wasu 'yan siyasa na take-taken yin magudin zabe, kuma bayan hatsaniyar an fasa kada kuri'a a wannan rumfa, amma rahotanni na cewa ana ci gaba da zabe a sauran sassa na birnin da ma jihar ta Filato.

15:22 Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na cewa akalla mutum guda ya rasa ransa sakamakon wata hatsaniya da ta kaure a wata rumfar zabe dake Unguwar Ali Kazaure a cikin birnin na Jos.

14:40 A sakon da Abdullahi Muhammad Maiyama ya aiko mana a Facebook, ya ce "mu dai garin Maiyama komai na gudana lami lafiya; fatan mu shi ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ba mu abin da muka zaba."

Hakkin mallakar hoto Abdulrazaq Yusuf
Image caption Mata sun fito domin zabe a Wukari na jihar Taraba

13:40 Bayanan da ke fitowa daga jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi a arewa maso yammacin Najeriyar na cewa ma'aikatan zabe sun fito a kan lokaci kuma komai na tafiya lafiya, sai dai masu kada kuri'a basu fito sosai ba idan aka kwatanta da zaben shugaban kasa, in ji wakilinmu Haruna Shehu Tangaza.

13:32 "Mu dai a nan mazabarmu ta Kanguri a karamar hukumar Gamawa jihar Bauchi, har ila yau kaman lokacin zaben shugaban kasa ana samun matsala da na'urar tantance masu kada kuri'a wato card reader," in ji Sani Adamu Kanguri.

Abdulkadir Adamu Wuro-dabo, ya aiko mana cewa "Mu mutanen karamar hukumar Nafada a jihar Gombe ba a fito sosai ba sabo da matsalarmu ita ce rashin tsaro muna tsoron ka da a maimaita abin da ya faru a zaben shugaban kasa."

13:26 Sufiyanu Ibrahim G, ya aiko mana da wannan sakon ta shafinmu na Facebook "Mu dai a nan garin gatawa da ke jihar Sokoto akwai rumfuna biyu da aka samu mastalar card reader da har yanzu ba a fara tantance mutane ba."

Image caption Masu kada kuri'a a wata mazaba a Surulere ta Lagos

13:15 Jam'iyyar APC ta yi korafi zuwa ga jami'an tsaro a kan cewa ana kokarin tayar da rikici a wasu yankuna a jihohin Lagos da Ribas da kuma Ondo domin lalata harkokin zabe.

12:47 Salihu Umar Marasy ya aiko mana da wannan sakon ta shafinmu na Google + : "Mu a nan Yola ta Kudu jihar Adamawa, a anguwar Rumde Jabbi ana ci gaba da tantanci masu kada kuri'u, kuma komai na tafiya lami lafiya amma ba jama'a sosai".

12:41 A karamar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina, akwai rahotannin da ke cewa an samu hatsaniya kuma har izuwa karfe 12 na rana ba a soma tantance masu kada kuri'a ba kuma babu kayayyakin zabe.

Hakkin mallakar hoto APC Campaign Organistion
Image caption Janar Buhari a lokacin da ake tantance shi Daura
Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Shugaba mai barin gado, Goodluck Jonathan a lokacin da ake tantance shi

12:13 Abdul Abdul ya aiko mana sako a Facebook, yana cewa "A nan mazabata da ke GGSS Malumfashi Jihar Katsina, gaskiya abin Allah san barka domin kuwa tuni an tantance mu, lokaci kawai muke Jira mu kada kuri'unmu."

11:54 Wani a sansanin 'yan gudun hijira da ke Yarwa a birnin Maiduguri na jihar Borno, Ishaka Bama ya bayyana cewa an kusan kamalla tantance masu kada kuri'a amma kuma babu takardar kada kuri'a ta zaben gwamna.

11:26 Adamu Jumba Madara a shafinmu na Facebook ya ce "mu dai a nan a rumfar sakatariyar Madara da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi, sai misalin karfe 11:00 aka fara tantancemu."

Image caption Wadanda aka tantance a jihar Kaduna

11:23 Bayanai da wakilinmu Ishaq Khalid ya tattaro daga johohin Bauchi da Gombe na cewa an fara tantance masu kada kuri'u a tsare kamar yadda ya kamata, sai dai mutane ba su fito da yawa kamar zaben shugaban kasa ba.

11:18 Mai sauraron BBC Hausa a jihar Taraba, AbdurRazaq Yusuf Sangari ya aiko mana cewar a mazabar maman kato 1 da kuma 11 da ke karamar Wukari an tantance mutane lami lafiya babu matsala. A yayinda kuma a rumfar zabe ta kofar shishi da ke mazabar Puje, an soma kada kuri'a ba tare da tantance masu zabe ba, abin da ya janyo hatsaniya aka kuma fasa na'urar Card Reader.

11:01 Wakilinmu a Jigawa, Muhammad Annur Muhammad ya ba mu rahoton cewa a Dutse babban birnin jihar mata ba su fito domin kada kuri'a kamar yadda suka fito a zaben shugaban kasa ba. Sannan kuma a karamar hukumar Birniwa da farko an fuskanci matsalar na'urar 'Card Reader' amma daga bisani a kan shawo kan matsalar.

Hakkin mallakar hoto Abdulrazaq Yusuf
Image caption Jami'an zabe a Wukari na jihar Taraba

Sakonni daga Twitter:

@GodwinGodiya a shafinsa na Twitter ya ce "a nan Sapele jihar Delta, mutane basu fita zabe sosai ba."

@adnanjunaidu ya ce "a yanzu haka ana tantance jama'a a rumfar zaben mu da ke nurses quarters a jihar Bauchi, kuma komai na tafiya dai- dai."

10:37 Wakilin BBC Abdussalam Ahmad ya shaida mana cewa a mazaba ta 18 da ke unguwar Mba a yankunan Apara karamar hukumar Etche a jihar Rivers wasu 'yan bindiga sun je mazabar in da su ka bude wuta a sama tare da dukan malaman zaben su ka kuma kwace kayan aikin su ka gudu. Al'amarin ya tarwatsa ma'aikatan zabe da kuma mutanen da ke kan layi domin a tantancesu. A yanzu haka Malaman zaben na samun mafaka a hukumar zaben.

Image caption 'Yan kasuwa sun ci gaba da kasuwanci a garin Bauchi

10:23 Wakilinmu da ke Katsina Abba Muhammad ya shaida mana cewa babu jami'an tsaro a mafi yawan rumfunan zaben da ke jihar. Haka zalika ba bu jami'an tsaro a kan tituna kamar yadda hukumar 'yan sanda ta ce za a baza domin takaita zirga-zirgar jama'a, hakan ya jawo mutane na zirga-zirga tsakanin kananan hukumomi da yankuna.

10:20 "Mu a anguwarmu a Wauru Jabbe da ke karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, na'urar card reader na aiki sosai ba bu tangarda. Kuma komai na tafiya lami lafiya a cikin lumana," In ji Umar Adamu Chindo a sakonsa ta email da ya aiko mana.

10:15 Alhaji Sanda Muhammad Waziri daga karamar hukumar Geidam a jihar Yobe ya aiko mana ta wayar salula cewa a mazabu uku da ya ziyarta wato Unguwar Bolori da Tsaganyar kashi da kuma Kofar Ali Abba. Mutane basu fito ba sosai kamar yadda suka fito makonni biyu da suka wuce lokacin zaben shugaban kasa.

  • Sakonni daga BBC Facebook:

Ahmed India Gashu'a ya ce "A mazabarta ta garin Lamido makaranta da ke karamar hukumar Gashuwa a jihar Yobe, Malaman zabe sun zo da wuri har ma an fara tantance mutane kuma har zuwa yanzu ba a samu wata matsala da na'urar tantance mutane ba wato Card Reader."

Image caption Wasu matasa a Lagos suna kwallo a lokacin da ake gudanar da zabe

Ibrahim Aliyu Abubakar ya shaida wa BBC cewa "A nan mazabar unguwa uku kauyen Alu da ke jihar Kano, gaskiya mutane basu fito ba sosai amma komai yana tafiya dai-dai."Shi ma Ibrahim Mu'azzam Umar cewa ya yi "A gaskiya ba'a fito sosai ba a mazabar Kankarofi da ke jihar Kano."

09:56 Rahotanni daga Daura a jihar Katsina sun nuna cewa tun da misalin karfe 8:15 na safe ne, zababben shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari da matarsa, Hajiya Aisha suka je rumfar zabe ta Sarkin Yara A da ke Kofar Baru III, inda aka tantancesu. Sai mutane basu fito ba kamar yadda suka fito lokacin zaben shugaban kasa makonni biyu da suka wuce.

09:50@gimbakakanda a shafinsa na Twitter ya ce an soma tantance masu kada kuri'a a kananan hukumomi 25 na jihar Niger. A cewarsa kawo yanzu babu rahoton tashin hankali.

Image caption Mutanen da suka fito zabe a jihar Rivers ba suda yawa

09:44 A jihar Kaduna ma'aikatan zabe ba su isa a kan lokaci ba a mafi yawan mazabu, amma tun karfe 8 na safe mutane su ka hau kan layi suna jiransu.

*Sai da misalin karfe 9.15 ne tsirarun ma'aikatan su ka fara zuwa mazabunmu da wakilinmu Nurah Muhammed Ringim ya ziyarta. Yawan mutanen da su ka je mazabun I zuwa yanzu dai basu kai yawan na zaben shugaban kasa ba.

09:30 Wakilinmu a Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce an soma tantance masu kada kuri'a a kan lokaci. Mutane sun fito dama kuma babu matsalar amfani na'urar card reader. Kuma babu bata lokaci wajen tantance mutane a galibin mazabun da ya ziyarta. Amma akwai yanayi na hazo a birnin Kano abin da watakila zai bai wa jama'ar fitowa a kan lokaci tun da babu zafin rana.

Image caption Nurah Muhammed Ringim a Kaduna ya ce mutane na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

09:13 Abokin aikinmu Abba Muhammad Katsina ya bamu rahoton cewar galibin mazabun da ya ziyarta a sassa daban-daban na jihar Katsina, ana gudanar da aikin tattance masu kada kuri'a kuma mutane sun fito tun da safe domin a tantancesu.

09:00 Babu zaben gwamna a jihohin Ondo, Osun, Edo, Ekiti, Anambra, Bayelsa da kuma Kogi.

08:34 Wata mata daga unguwar jan bango a jihar Katsina, mai suna Fatima S Mohammed ta bamu rahoton cewa a mazabarta da ke Strolling Estate, na'urar card reader ba ta aiki. A don haka an soma fuskantar matsala wajen tantance masu kada kuri'a.

08:30 Jihohin da takarar za ta fi zafi su ne; Lagos a tsakanin Akinwumi Ambode na APC da Jimi Agbaje na PDP, da kuma Ribas tsakanin Dakuku Peterside na APC da Nyesom Wike na PDP sai kuma jihar Kaduna tsakanin Mukhtar Ramala Yero na PDP da kuma Nasir El-Rufai na APC.

Image caption Daya daga cikin hotunan da Umar Shehu Elleman ya aiko mana daga Lagos

08:25 Jam'iyyar APC na fatan samun kuri'u masu yawa bayan da dan-takararta na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kayar da Shugaba Goodluck Jonathan a zaben kujerar shugabancin kasar makonni biyu da suka gabata.

08:02 Kwamishin zabe na jihar Bayelsa, Baritor Kpagih ya ce an jinkirta zaben ne a mazabu takwas saboda rashin kayayyakin zabe.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwatin zabe na gwamna na da jan murfi a yayinda na 'yan majalisa ke da murfi baki

07:54 Wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed wanda yake birnin Fatakwal a jihar Ribas, ya ce an dage zabe a mazabun 'yan majalisar dokoki takwas daga cikin 24 na jihar Bayelsa. Hukumar zabe ta ce za a gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa watau 18 ga watan Afrilu.

07:47 Wakilinmu na Kaduna, Nurah Muhammad Ringim ya ce galibin rumfunan zaben da ya zagaye, ya ga mutane sun fito suna jira a rumfunan zaben, sai dai galibin jami'an zaben da kayayyakin zabe ba su isa rumfunan. A cewarsa, adadin mutanen da suka fito basu kai yawan na zaben shugaban kasa ba.

07:42 Wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce izuwa karfe bakwai saura 'yan mintuna, mutane ba fito sosai ba zuwa rumfunan zabe musamman idan aka kwatanta da yadda mutane suka fito kwansu da kwarkwata a lokacin zaben shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Hukumar zaben Nigeria ta ce ta shirya domin yin zabe mai adalci

07:40 Hukumar zaben Nigeria- INEC ta ce mutane 6,050 ne ke yin takarar kujerun gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a zaben na yau.

07:35 Wakilinmu Umar Shehu Elleman a birnin Lagos ya ce mutane sun soma fitowa zuwa rumfunan zabe a wurare da dama a Lagos duk da cewa sai karfe takwas za a soma tantance masu kada kuri'a.