An soma tattara sakamakon zaben gwamnoni

Image caption Mata sun fito da dama domin kada kuri'a a Kaduna

An soma tattara sakamakon zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki a Nigeria, inda ake hasashe jam'iyyar APC ce za ta fi samun galaba.

Bayanai sun nuna cewar zaben ya fi zafi ne a jihohin Lagos da kuma Ribas.

Ana sa ran za a samu cikakken sakamakon zaben gwamnonin da kuma na 'yan majalisar a ranar Lahadi.

A makonni biyu da suka wuce ne Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya doke Goodluck Jonathan na PDP a zaben shugaban kasa.

Jam'iyyar PDP ta shiga zaben na ranar Asabar ne da gwamnoni 21 a yayinda APC ke da gwamnoni 14.

Gwamnoni na da karfin fada a ji a siyasar Nigeria inda wasu jihohi ke da kasafin kudi fiye da na wasu kananan kasashen Afrika.