Bamu damu da kin shigar Pakistan yaki ba- Saudiyya

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Hare haren da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ba sa yin tasiri akan 'yan tawayen Houthi

Saudi Arabiya ta ce shawarar da Pakistan ta yanke na kin shiga gamayyar sojojin da ita Saudiyyan ke jagoranta a Yemen ba zai takaita farmakin da take kaiwa 'yan tawayen Houthi ba.

Rundunar sojin Saudiyyan tace dakarun Pakistan din, da rawa kawai zasu taka na nuna goyan baya, sannan kuma ana samun cigaba sosai a farmakin da ake kaiwa 'yan tawayen Houthin.

Sai dai wakiliyar BBC ta ce rashin shigar Pakistan wannan yaki wannan wani babban komabaya ne ga daular ta 'yan Sunni, yayinda a karon farko take jagorantar gamayyar sojojin kasashen dake yaki da 'yan Houthi a Yemen.