Zabe2015: 'Yan Najeriya na dakon sakamako

Image caption 'Yan Najeriya masu kada kuri'a

A Najeriya, jama'ar kasar na ci gaba da dakon bada sanarwar zabukan gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi da aka gudanar ranar Asabar.

Hukumar zaben kasar INEC ta gudanar da zaben gwamnonin ne a jihohi 29, sannan aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin jihohin a jihohi 35.

Rahotanni sun nuna cewa ba a ci karo da matsaloli sosai ba kamar yadda aka gani a zaben shugaban kasar kimanin makonni biyu da suka gabata. Inda na'urar tantance masu kada kuri'a ta bada matsala a wasu wurare, sannan aka samu tsaikon kai kayan zabe a wasu wurare.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa jama'a basu fita sosai ba, kamar yadda aka gani a zaben shugaban kasa.

A yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zabukan, hukumar zaben ta ce tana sa ran sanar da sakamakon cikin sa'o'i 48 da kammala zabukan.

An samu 'yan hatsaniya a wasu jihohi a lokacin zabukan gwamnonin dana 'yan majalisun, lamarin da ya haifar da rasa rayuka.