Kenya ta yi gargadi kan 'yan gudun hijirar Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kenya na fargabar ana daukar mayakan Al-Shabab a sansanin Dadaab

Majalisar dinkin duniya ta ce bata sami wani umarni daga gwamnatin Kenya ba a hukumance, na rufe wani sansanin 'yan gudun hijira da ya kasance gida ga dubban 'yan Somalia.

A ranar asabar ne mataimakin Shugaban Kasar Kenya William Ruto ya ce ya baiwa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniyar watanni uku, domin ta rufe sansanin Dadaab, sannan ta tasa keyar 'yan gudun hijirar dake sansanin zuwa Somalia.

Idan ba haka ba, ya ce Kenya za ta yi gaban kanta.

Wasu 'yan siyasar Kenyan dai sun yi imanin cewa sansanin ya kasance wani waje da ake daukar mayakan Al-Shabab na Somalia, kungiyar data halaka dalibai kusan 150 a wata jami'a a kasar Kenya a makon da ya gabata.

Kenya na fuskantar matsin lamba sosai saboda karuwar hare- haren da mayakan Al-Shabab suke kaiwa a cikin kasar, a saboda haka ne take sanar da wasu jerin matakai akan 'yan Somalia