Jam'iyyar APC ta lashe zabe a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akinwumi Ambode zai gaji Babatunde Fashola

Jam'iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Lagos, bayan da dan takararta Akinwumi Ambode ya doke Jimi Agbaje na jam'iyyar PDP.

Ambode na APC ya samu kuri'u 811,994 a yayinda Agbaje na PDP ya samu kuri'u 615, 788.

Tuni Mr Agbaje ya kira Ambode domin taya shi murnar lashe zaben.

A jihar Akwa Ibom da ake ta cece-kuce kan zaben, hukumar zabe ta sanar da Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Jami'in INEC a Uyo, James Epoke ya ce Mr. Emmanuel ya samu kuri'u 996, 071 inda ya doke Umana Umana na APC wanda ya samu kuri'u 89,865.

INEC ta sanar da Ifeanyi Ugwuanyi na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Enugu.

Babban jami'in da lura da zaben, Farfesa Hilary Edoga ya ce Ugwuanyi ya samu kuri'u 482,227 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Mr Okey Ezea na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 43,839.