Mayakan IS sun yi rusau a garin Nimrud

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai dadaddun kayayyakin tarihi a Nimrud da kuma gumaka

Wani bidiyo da mayakan IS suka saka na nuna masu ikirarin yin jihadin sun lalata birnin Nimrud mai cike da tarihi.

Birnin dai, na daya daga cikin manyan wuraren da ake da kayayyakin tarihi a Iraqi.

Hotunan bidiyon sun nuna mayakan su na lalata abubuwa na tarihi ta hanyar amfani da guduma da wasu karafuna

Sannan su ka yi amfani da manyan motoci na rusau wajen tattake barugazan abubuwan da suka lalata , da kuma fashewar abubuwa masu karfi.

Kungiyar IS ta kare matakin data dauka a matsayin wani bangare na yakin da take yi da abinda ta bayyana da gumaka na karya.

A lokacin da aka samu rahotan irin ta'adin da mayakan suka yi a Nimrud da farko a cikin watan Maris, Majalisar dinkin duniya ta yi allawadai da matakin, ta na mai bayyana shi da laifi na yaki