APC ta lashe zaben gwamna a Jihar Jigawa

Image caption Jam'iyyar APC

A jihar Jigawa dake arewacin Najeriya, hukumar zabe ta bayyana Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar na jam'iyyar APC a matsayin sabon zababben gwamnan jihar.

Hukumar ta ce Alhaji Badaru Abubakar ya samu kuri'u 648, 045 inda ya doke sauran abokan hamayya na jam'iyyar PDP Malam Aminu Ringim da Yaro Sardauna Elleman na jam'iyyar APGA da kuma Musa Murtala Galamawa na Jam'iyyar NCP

Mal Aminu Ringim ya samu kuri'u 479, 447 yayinda Yaro Sardauna Elleman ya samu kuri'u 1997 sannan Musa Murtala Galamawa ya samu kuri'u 1394.

Da misalin karfe 3:45 na daren Lahadi aka sanar da sakamakon.

A jihar Kebbi, hukumar zaben ta bayyana Sanata Atiku Abubakar Bagudu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.