Masari, Ajimobi da Tambuwal sun samu nasara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zababbun gwamnoni a jihohin Katsina da Sokoto

Tsohon shugaban majalisar wakilan Nigeria, Aminu Bello Masari ya lashe zaben gwamna a jihar Katsina.

Hukumar zaben kasar ce ta sanar da Masari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya samu kuri'u mafi rinjaye inda dan takarar jam'iyyar PDP, Musa Nashuni ya zama na biyu.

A jihar Oyo da ke kudancin kasar kuwa, Sanata Abiola Ajimobi ya kafa tarihi a matsayin wanda ya yi tazarce a kujerar gwamnan jihar bayan da hukumar zabe ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ajimobi na jam'iyyar APC wanda shi ne gwamna mai ci a yanzu, ya samu galaba a kan tsofaffin gwamnonin jihar biyu watau Rashidi Ladoja na jam'iyyar Accord da kuma Adebayo Alao-Akala na jam'iyyar Labour.

Shi ma shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben gwamnan jihar Sokoto.

Tambuwal ya shi gaban surikinsa Sanata Abdullah Wali na jam'iyyar PDP.

Sauran da suka lashe kujerun gwamna sun hada da Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, Nasir El-Rufai a jihar Kaduna da kuma Ibikunle Amosun na jihar Ogun.