APC ta yi nasara a zaben Niger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu ma ya sha kaye a yunkurinsa na zama Dan Majalisar Dattawa

Dan takarar gwamnan jihar Niger a karkashin jam'iyyar PDP, Umaru Nasko ya taya abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Abubakar Sani Bello murnar lashe zaben jihar.

Hukumar zaben jihar dai ta ayyana Abubakar Sani Bello a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Niger.

A sanarwar da mai magana da yawun Umaru Nasko ya fitar, ya ce ya karbi kaddara bisa matakin da jama'ar jihar suka dauka na zabar abokin hamayyarsa, yana mai yin kira a gare shi da ya yi ayyukan ci gaban jihar tasu.

Ko da makonni biyu da suka wuce, dan takarar kujerar Majalisar Dattawa, wanda kuma shi ne gwamnan jihar, Alhaji Mu'azu Babangida Aliyu na jam'iyyar PDP ya sha kaye a hannun Mr David Umaru na jam'iyyar APC.