Iran ta hana 'yan kasarta zuwa Umara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Iran ta ce 'yan kasarta ba za su sake zuwa Umrah ba idan ba a hukunta mutanen da suka yi luwadi da mahajjatan ba.

Kasar Iran ta hana 'yan kasarta zuwa Saudiyya domin yin Umara a daidai lokacin da dangataka ta yi tsami a tsakaninsu sanadiyar rikicin Yemen.

Iran ta ce ta dauki matakin ne bisa zargin da ta yi cewa jami'an tsaron Saudiyya sun yi luwadi da 'yan Iran guda biyu da suka je kasar domin yin Umara a watan jiya.

Ministan da'a na Iran ya ce ba za su bar 'yan kasar su sake zuwa Umara ba sai Saudiyya ta hukunta mutanen da suke da hannu a wajen wulakanta 'yan kasarta.

Kimanin Iraniyawa 500, 000 ne ke zuwa Saudiyya a kowacce shekara domin yin Umara.

A karshen makon jiya 'yan kasar ta Iran sun yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Tehran domin nuna kyama kan lalatar da jami'an tsaron Saudiyyar suka yi wa 'yan uwansu.