Nigeria: An kafa kwamitin karbar mulki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar 29 ga watan Mayu za a mika mulki ga sabuwar gwamnatin Buhari

Gwamnatin Najeriya mai barin-gado ta kaddamar da kwamitin da zai shirya yadda za ta mika ragamar mulkin kasar ga sabuwar gwamnati mai jiran-gado.

Kwamitin na karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasar Mohammed Namadi Sambo tare da Sakataren gwamnatin tarayya da wasu ministoci da masu ba shugaba Jonathan Shawara a zaman wakilansa.

Kwamitin zai karbo rahotanni daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati kan yadda suka gudanar da ayyukansu cikin shekaru shida na mulkin Jonathan.

Daga nan kuma 'yan kwamitin za su zauna da takwarorinsu na gwamnati mai jiran-gado su ba su bayanai da amsa tambayoyi kan abubuwan da za su bukata su sani.

Kwamitin zai kuma tsara abubuwan da Shugaba Goodluck mai barin-gado zai gabatar wa mai gadonsa Janar Muhammadu Buhari yayin mika mulki.