'Yan sanda sun kama mutane 13 a Zamfara

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Dan Sanda

Rundunar 'yan sandar jihar Zamfara ta tsare mutane goma sha uku sakamakon zanga-zangar da aka yi a jihar bayan zaben gwamna da na 'yan majalisar dokoki.

Zanga-zangan ya faru ne bayan da magoya bayan 'yan adawa sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaben, wanda hukumar zaben jiha ta ce gwamna Abdul Aziz Yari ne ya sake lashewa.

Yan adawan sun yi ta zanga-zangar ne da yammacin ranar Lahadi lamarin da ya kawo hatsaniya a Jihar ta Zamfara.

Rundunar 'yan sandar ta ce tana gudunar da bincike akan mutanen da ta kama, kuma za ta hukunta duk wanda ta samu da tayar da zaune tsaye.