Sudan: Yau ake gudanar da zaben Shugaban Kasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben Sudan

Sudan na gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na 'yan majalisu a ranar Litinin .

Shugaba Omar al Bashir ya dauko hanyar yin nasara cikin ruwan sanyi, bayan da mafiyawancin manyan jam'iyyun adawar kasar suka yanke shawarar kauracewa zaben, bayan da sukayi korafin cewa ana musguna musu a siyasance.

Shugaba Bashir wanda ya hau mulki a wani juyin mulki a shekarar 1989, ya ce zai inganta tattalin arzikin kasar.

Kotun manyan laifuka ta duniya dai na neman Omar al-Bashir ruwa a jallo bisa zarge zargen kisan kiyashi.

Wannan shine zaben Sudan na duk kasa na farko, tun lokacin da bangaren Kudancin Sudan din ya samu 'yancin kai a shekarar 2011.

Kasashen yammacin duniya da dama kamar Amurka da Burtaniya, sun ce ba za'a gudanar da sahihin zabe ba