UNICEF: Yara dubu 800 ne suka tsere daga Nigeria

Hakkin mallakar hoto .
Image caption 'Yan boko Haram sun kuma yi awon gaba da yara

Asusun kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya ya ce kananan yara 800,000 ne aka tilasta wa tserewa daga gidajensu sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria ke kai wa.

UNICEF ta ce yawan yaran da suka tsere ya kara ninkawa a cikin kasa da shekara guda, inda yara da dama na Nigeriar suka ketara iyaka cikin kasashen Chadi da Niger da Kamaru domin tserewa tashe- tashen hankula.

An saki rahoton ne yayin da ake cika shekara guda da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 daga garin Chibok

Malala Yousufzai ta aike da sako zuwa 'yan matan Chibok

A yayin da ya rage kwana daya 'yan matan Chibok su cika shekara daya cif a hannun kungiyar Boko Haram, yarinyar nan mai fafutukar samarwa da yara mata damar yin karatu, Ms Malala Yusufzai ta gabatar da wani sakon murya domin karfafa gwiwa ga 'yan matan na Chibok a duk inda ake tsare da su.

A cikin sakon, Ms Malala ta bukaci hukumomi a Najeriya da sauran kasashen duniya da su kara azama domin ceto 'yan matan na Chibok.