An yanke wa tsoffin sojin Amurka hukunci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kotun ta kuma yi hukuncin cewa wasu farar hula uku da aka kashe,a Irakin an kashe su ne bisa doka.

Wani alkalin tarayya a Washington ya yanke hukuncin zaman gidan yari a kan wasu masu aikin tsaro na kamfanin harkokin tsaro na Blackwater su hudu, kan kisan wasu farar hula 14 'yan Iraki da kuma raunata wasu 17, a 2007.

An yanke wa Nicholas Slatten hukuncin rai da rai, yayin da Dustin Heard da Evan Liberty da Paul Slough kowannensu ya samu hukuncin shekaru talatin talatin a gidan maza.

Alkalin ya ki amincewa da bukatar jinkai da lauyoyin da ke kare su suka bukata, haka kuma ya yi watsi da bukatar lauyoyi masu gabatar da kara ta yi musu hukunci mai tsanani, inda ya yanke musu hukunci mafi kankanta da doka ta tanada.

An samu dukkanin mutanen hudu wadanda tsoffin sojojin Amurka ne da laifi a watan Oktoba da ya wuce.