Shekara daya da sace 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace a ranar 14 ga watan Aprilun 2014

A ranar Talatan nan ne 'yan matan nan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daga makarantar sakandaren garin Chibok na jihar Borno a gabas maso arewacin Najeriya ke cika shekara guda da sacewa.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne dai wasu 'yan bindiga suka kai hari a makarantar Sakandaren inda suka yi awon gaba da dalibai mata fiye da dari biyu.

A cewar wadanda suka shaida lamarin, wanda kungiyar Boko Haram ta dauki alhakinsa, mayakan sun je makarantar ne a cikin dare.

Ko da yake wasu daga cikin 'yan matan sun kubuta, har yanzu 219 daga cikinsu ba a san halin da suke ciki ba.

Kungiyoyi da kasashen daban-daban na duniya na ci gaba da yin kira wajen ganin an ceto 'yan matan, amma har yanzu kamar an shuka dusa duk da ikirarin da gwamnati ta sha yi cewa za ta ceto su.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service