An kashe mutane biyar kan launin fata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan kasar Afrika ta kudu tana bakin kokarinta na hana masu kai hare-haren kin jinin lauynin fata.

An kashe mutane biyar sakamakon hare-haren da masu nuna wariyar launin fata suka kai a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu.

'Yan sanda sun kara zage dantse wajen tsaurara matakan tsaro domin hana kai irin wadannan hare-hare a shagunan 'yan kasuwa baki haure.

An tilasta wa mutane sama da dari sauya wuraren zama a dalilin irin wadannan hare-hare, kuma kasar Malawi ta ce za ta debo 'yan kasarta wadanda suka rasa muhallinsu a Afrika ta kudu.

Shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, ya kyamaci wadannan hare-hare, kuma ya kafa kwamitin da zai yi kokarin dawo da bin doka da oda a birnin na Durban.