EU na tuhumar Google

Image caption Kungiyar EU ta ce kamfanin Google din kansa kawai ya sani tare da keta dokokinta.

Kungiyar Tarayyar Turai, EU ta tuhumi shafin matambayi ba ya bata na Google da yin ka-ka-gida a kasuwar intanet.

Hakan ya biyo bayan binciken da EU din ta shafe shekaru biyar tana yi domin tabbatar da zargin.

Wata babbar jami'ar EU, Margrethe Vestager, ta ce ta damu da yadda kamfanin Google din ke kokarin ganin ci gaban kansa kawai tare da keta dokokin Tarayyar Turai.

EU ta kuma kaddamar da wani bincike a kan manhajar Android ta Google.

Shafin Google dai shi ke samar da kashi 90 cikin 100 na bayanan na ake nema a shafin intanet dangane da EU

Har yanzu dai ba a ji ta bakin Google ba kuma makonni 10 kacal kamfanin ke da shi domin ma yar da martani.