Layin mai: Dillalai na zargin gwamnati

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan bumburutu na cin kasuwarsu sakamakon karancin man

Dillalan man fetur sun dora alhakin karancin man da ya haddasa dogayen layukan ababan hawa a gidajen mai na wasu jihohi da Abuja a kan kin biyan su bashi da gwamnati ta yi.

Kafin zabukan da aka gudanar a kasar, gwammnati ta ce karancin mai ya zama tarihi bayan da ta ce ta biya dillalan man kudin da suke binta.

To amma yanzu dillalan na cewa, gwamnatin ba ta cika wannan alkawari ba ne shi ya sa matsalar karancin man ta sake kunno kai.

Sai dai kuma mai magana da yawun kamfanin mai na Najeriyar, NNPC, Muhammad Umar ya musanta maganar.

Ya ce idan da gaskiya ne, da ba a Abuja kadai za a rika ganin dogayen layukan ababan hawa ba.

Kuma kudaden da gwamnati ta yi musu alkawari a baya tuni ta biya su.