Birtaniya: Ana cire hotunan batsa daga intanet

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ana cire hotunan batsa daga kan intanet a Birtaniya

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Birtaniya ta ce ta taimaka wajen gano da cire hotunan batsa masu yawa a shekarar 2014.

Kungiyar mai suna Internet Watch Foundation(IWF) ta ce a shekarar 2014 kawai ta samu nasarar kawar da hotunan har dubu 31,266.

IWF ta ce akan samu hotuna masu motsi da marasa motsi sama fiye da daya akan kowane adireshi.

Kungiyar ta samu nasarar yin hakan ne bayan da manyan kamfanonin kasar masu samar da tsarin intanet suka ba ta tsabar kudi har fan miliyan daya a tsawon shekaru hudu don yaki da hotunan na batsa.