Ebola: Za a bude makarantu a Saliyo

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Za a bude makarantu a kasar Sierra Leone

A yau Talata ne za a bude makarantu a kasar Saliyo tun bayan da aka rufe su a watan Yuli sakamakon barkewar cutar Ebola.

Tun a farkon shekaran nan ne aka bude makarantu a sauran kasashen Yammacin Afrika, wato Guinea da Liberia da su ma annobar ta shafa.

Sai dai hukumar lafiya ta duniya ta ce har yanzu annobar ta Ebola babbar barazana ce ga duniya.

Alkaluman mako-mako na baya bayan nan na sababbin wadanda suka kamu da cutar sun nuna mutane 30 ne suka kamu da cutar a Guinea da Saliyo, sabanin daruruwa da ake samu a lokacin tsananin annobar ta Ebola.