An bude makarantu a Saliyo

Hakkin mallakar hoto
Image caption An bude makarantu a Saliyo

A kasar Saliyo, an bude makarantu a karon farko tun bayan barkewar cutar Ebola a shekarar 2014, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da rufe makarantu a wancan lokacin.

A Saliyo, makarantu na ci gaba da yi wa dalibai marhabin da dawo tun lokacin da aka tursasa su rufewa saboda barkewar cutar Ebola.

Yara miliyan biyu na komawa makarantu, sai dai 9,000 daga cikin su sun zama marayu saboda annobar.

Mallamai suna ci gaba da koyawa yara hanyoyi na musamman na kariya daga yaduwar cutar ta Ebola saboda an samu sababbin rahotonnin yaduwar cutar.

Tun farkon wannan shekarar, kasashen Yammacin Africa na Guinea da Laberiya -- inda cutar ta yadu -- suka bude makarantu.

Kungiyar kula da lafiya ta duniya ta ce har yanzu dai Ebola cuta ce da ke bukatar kulawar gaggawa a duniya.

Ta kara da cewa kawo yanzu cutar ta kashe mutane fiye 10,000.