Kamaru: Gwamnati ta yi karar jaridu bisa kage

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ke nan

Kakakin gwamnatin Kamaru, Isa Ciroma Bakary, ya shigar da karar wasu jaridun kasar masu zaman kansu guda uku gaban hukumar sadarwa da yada labaru bisa tuhumar jaridun kan wallafa labaran kage.

Jaridun dai sun wallafa labari kan lafiyar shugaban kasar ta Kamaru, Paul Biya da ake ganin ba gaskiya ba ne.

Haka kuma jaridun sun wallafa hoton shugaban kasar na bogi a shafin intanet a inda aka nuna shi yana karrama sojojin da suka kwanta dama a lokacin da suke yaki da 'yan Boko Haram.

Kakakin gwamnatin ya ce shugaban kasar ba ya Kamaru a lokacin da jaridun suka ce ya karrama sojojin saboda haka labarin kanzon kurege ne