'Yan matan Chibok suna raye- Salkida

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace

Wani dan jarida da aka san shi da samun kwararan bayanai daga kungiyar Boko Haram, ya shaida wa BBC cewa 'yan matan Chibok fiye da dari biyu da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke rike da su, suna nan da rai kuma cikin koshin lafiya.

A wata hira da ba kasafai yake irinta ba, dan jaridar Ahmed Salkida wanda ya jima yana ba da rahotanni a kan aikace-aikacen 'yan Boko Haram, ya ce 'yan matan na Chibok, suna da matukar muhimmanci ga 'yan kungiyar.

Hakan ya ce ba ya rasa nasaba da karbar musulunci da 'yan matan suka yi bisa akidar 'yan kungiyar, a don haka shugabannin kungiyar ne suke kula da su da kansu.

Ahmed Salkida ya kara shaida wa BBC cewa wasu daga cikin 'yan matan na Chibok sun auri 'ya'yan kungiyar kuma suna tare da su.

Wadanda kuma ba su yi aure ba suna ware a waje daya