Tattalin arzikin Sin ya samu koma baya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tattalan arzikin Sin na yin tafiyar hawainiya

Alkaluman da gwamnatin Sin ta fitar sun nuna cewar tattalin arzkin kasar -- wanda shi ne na biyu a duniya -- yana yin tafiyar hawainiya.

Tattalin arzikin kasar ya karu ne kawai da kashi bakwai cikin 100 a watannin ukun farko na wannan shekarar, idan aka kwatanta shi da yadda yake bara warhaka.

Wannan ne karo na farko da tattalin arzikin kasar ya fi fuskantar koma baya a cikin shekara 6.

Gwamnatin Sin ta sha alwashin rage yadda tattalin arzikin kasar ke bunkasa saboda samun damar ci gaba mai dorewa a kasar.

Amma masu sharhi sun nuna damuwar su saboda suna ganin cewa tattalin arzikin kasar zai iya samun koma baya fiye da yadda yake a yanzu.