EU za ta hukunta Google

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption EU za ta hukunta Google

Ana sa ran cewa nan ba da jimawa ba tarayyar turai wato EU za ta sanar da irin matakin da za ta dauka akan kamfanin Google bisa tuhumar nuna son kai wajen ba wa masu amfani da intanet dama su yi amfani da manhajarsa cikin sauri fiye da sauran kamfanoni.

Kwamishina mai kula da sashen gasar tallata hajar kamfanoni ta EU, Magrethe Vestager ce za ta sanar da matakin a ranar Laraba.

Hakan kuwa yana nuni ne da irin yanda aka ba wa korafe-korafen da kamfanoni ke yi akan Google din.

Kamfanin na Google dai yana mamaye kasuwar intanet a nahiyar turai da kaso 90 cikin dari.