Huawei ya fito da sabuwar waya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Huawei ya fito da sabuwar sanfirin waya

kamfanin Huawei ya fito da sababbin wayoyi samfirin P8 masu dauke da naurar daukar hotuna masu motsi da marasa motsi da kwararru za su iya amfani da su.

Kamfanin ya ce wayyoyin suna dauke da fasahar daukar hotuna masu inganci.

Sai dai duk da wannan nasara, masu sharhi sun ce har yanzu kamfanin yana da sauran tafiya a gabansa.

Amma kuma a baya bayan nan kamfanin ya matukar burge kwararru bayan da ya fito da sabon samfirin agogo mai aiki kamar wayar komai da ruwanka.