Italy: Jirgi ya kife da 'yan cirani 400

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kwale-kwale ya kife da 'yan cirani a Roma

Kusan 'yan cirani 400 ne ake fargabar ruwa ya ci, lokacin da kwale kwalensu ya nutse a kan hanyarsu ta Libya zuwa Italiya

Hadarin na baya bayan nan dai ya faru ne bayan da jirgin mai dauke da mutane 550 ya tuntsire kwana daya bayan ya bar kasar Libya a yayin tsallaka tekun Bahar Rum.

Mai magana da yawun kungiyar agazawa yara ta Save the Children, Carlotta Villini, ta gaya wa BBC cewa, sama da yara 400 sun isa Italia a cikin kwanaki uku.

Kungiyar ta ce mafi yawancin wadanda aka ceto matasa ne koma ace kananan yara.