Gobara ta tashi a wani babban gini a Lagos

Hakkin mallakar hoto Lagos
Image caption Gobara ta tashi a wani babban gini a Lagos.

Gobara ta tashi a wani fitaccen gini da ake kira Mamman Kontagora House, a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya.

Mamman Kontagora House gini ne mai bene hawa 15.

Wakilinmu na Lagos ya bayyana mana cewa gobarar ta tashi ne da safiyar ranar Laraba, kuma a yanzu haka ginin na ci da wuta.

Jam'ian kashe gobara sun isa wurin, suna kuma kokarin kashe wutar, amma kawo yanzu sun gaza sarrafa na'urar da za ta kashe wutar.

Mutane sun fiffito sun yi cirko-cirko suna kallon yadda ma'aikatan kashe gobarar za su shawo kan wutar.

Mamman Kontagora House tsohuwar ma'aikatar ayyuka ce, yana kuma makwabtaka ne da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki da bankuna.