Mali: An kai wa Sojin hadaka hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mali na fama da tawayen masu da'awar tsananin kishin Islama

Rahotanni daga Mali na tabbatar da wani harin kunar-bakin-wake da wasu mutane suka kai, kan sojin Majalisar dinkin duniya, wanda ya hallaka farar hula uku da jkkata sojoji 16.

Mutanen wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kai harin ne a ranar Laraba a sansanin sojojin shiga tsakani na majalisar dinkin duniya da ke kusa da Gao a Malin.

A sanarwar da rundunar ta bayar, wadda ta ce motar maharan ta tarwatse ne a kofar shiga sansanin sojin, ta ce daga cikin sojoji 16 da suka ji raunaku, tara na Nijar ne.

A watannin da suka gabata sojojin Nijar tara ne da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Malin suka mutu a kwantan baunar da aka yi musu.