Shugaba Goodluck Jonathan ya yi watsi da gyaran tsarin mulki

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sake mayar wa majalisun dokokin kasar kudirin dokar da ya kunshi wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaban kasar ya ki rattaba hannu a kan kudirin ne bisa zargin cewa 'yan majalisar sun taka ka'ida wajen yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai wasu 'yan majalisar sun ce ba su gamsu da hanzarin da shugaban Najeriyar ya bayar ba.