Rigingimu sun kare a Pilato — Lalong

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Jihar ta sha fama da matsaloli a karkashin mulkin gwamna Jonah Jang mai barin gado

Sabon zababben gwamnan jihar Pilato da ke Najeriya, Simon Lalong ya sha alwashin kawo karshen rikice-rikicen addini da na kabilanci da jihar ke fama da su fiye da shekaru 15.

Al'amarin ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkata daruruwan mutane.

Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen hadin kan kabilun da ke jihar guda 52.

Mr Lalong ya hakan zai taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankulan.

A karshen makon jiya ne jam'iyyar APC ta ci zaben gwamnan jihar ta Pilato inda ta ka da jam'iyyar PDP da ta dade tana mulki.