Amurka ta jaddada bukatar sakin matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yau fiye da shekara guda ke nan tunda Boko Haram ta sace 'yan matan Chibok.

Amurka ta jaddada bukatar sakin 'yan matan makarantar Chibok fiye da 200 wadanda kungiyar Boko Haram ta sace shekara guda da ta wuce.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin kasar, Marie Harf, ta fitar ranar Talata ta ce "ya kamata a gaggauta sakin dukkanin mutanen da kungiyar Boko Haram ta sace -- ciki har da 'yan matan Chibok-- ba tare da gindaya wani sharadi ba".

Marie ta tabbatar da cewa har yanzu dakarun Amurka na musamman suna Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya inda suke taimakawa a yunkurin da ake yi na kubutar da 'yan matan na Chibok.

A ranar Talata shugaban Najeriya mai jiran-gado, Janar Muhammadu Buhari, ya ce ba zai yi alkawari kai-tsaye cewa zai dawo da 'yan matan gida ba.

Sai dai ya sha alwashin zai zage dantse wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram fiye da gwamnatin Goodluck Jonathan.