Boko Haram: Jonathan ya ki amincewa da MDD

Image caption Shugaba Goodluck ya ce, Najeriya ba ta bukatar dakarun Majalisar dinkin duniya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya nemi Majalisar Dinkin Duniya ta sa hankali wajen taimaka wa kasar sake gina al'umomin da rikicin Boko Haram ya shafa maimakon tura rundunar sojin hadin gwiwa kasar.

Shugaba Jonathan ya yi wannan kalamin ne ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da wakilan majalisar na musamman a tsakiya da yammacin Afrika Mohammed Ibn Chambas da Abdoulahi Bathily a Abuja.

Mr Jonathan ya ce bai kamata majalisar ta yi amfani da sashe na bakwai na kundin ayyukanta ba, wanda ya tanadi amfani da karfin soji wajen wanzar da zaman lafiya don kai wa Najeriya dauki.

Ya ce, a maimakon haka, kamata ya yi a yi amfani da sashe na takwas na kundin majalisar, wanda ya bukaci aiki da kungiyoyin kasashe irin su,AU, ta Tarayyar Afrika, wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya, domin sun isa a matsalar Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Shi kuwa jakadan majalisar dinkin duniyar, Muhammad Ibn Chambas, ya ce suna rangadin kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa ne, a Yammaci da tsakiyar Afrika.

Ya kuma yaba wa shugaban na Najeriya kan amincewa da sakamakon zaben kasar.

Sannan ya bukaci sauran shugabannin Afrika da su yi koyi da hakan.