Ma'aikatan jiragen sama na yajin aiki a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan suna son gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Ma'aikatan da ke bai wa jiragen sama hannu a Najeriya sun fara yajin aiki ranar Alhamis.

Hakan dai ya sa fasinjoji a dukkanin filayen jiragen saman kasar suna ta ragaita.

Kakakin hukumar da ke kula da kula da jiragen sama ta kasar, Yakubu Dati ya ce jiragen da ke safara a cikin kasar kawai ba sa yin cikakken aiki saboda yajin aikin.

Sai dai ya ce jiragen da ke fita zuwa kasashen waje na ci gaba da yin jigila domin yajin aikin bai shafe su ba.

Kungiyar ma'aikatan da ke bai wa jiragen sama a hannu dai ta bukaci gwamnatin kasar ta inganta yanayin ma'aikatanta, sai dai har yanzu ba ta yi hakan ba.