Zanga-zanga a kan kin jinin baki a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane ne za su gudanar da zanga-zangar kan kin jinin baki.

Dubban mutane ne ke gudunar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Durban na Afrika ta kudu domin bijirewa kin jinin bakin da 'yan kasar ke yi.

Masu zanga-zangar -- wadanda suka kai 10, 000 -- na nuna goyon baya ga 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar.

'Yan kasar ta Afrika ta kudu sun kashe a kalla mutane biyar, sannan suka sace kayayyaki a kantunan 'yan kasashen waje da ke kasar a makon nan.

A birnin Johannesburg, 'yan kasashen Habasha da Somalia da sauran kasashen Africa sun rufe shagunansu saboda gudun kada a yi musu sata.

Ana zargin Basaraken gargajiya da rura wutar rikicin

Shugaban kasar Jacob Zuma ya yi tur da hare-haren da ake kai wa mutanen, kuma ana sa rai zai yi wa majalisar dokokin kasar jawabi idan anjima a kan lamarin.

Ana zargin fitaccen Basaraken gargajiya na kabilar Zulu da rura wutar kin jinin baki, sai dai ya musanta zargin.

'Yan kasar sun yi zargin cewa baki sun kwace dukkanin ayyukan da suka kamata a ba su, shi ya sa a yanzu kashi 24 cikin 100 na 'yan kasar ba su da aikin yi.

Dubban 'yan kasashen waje -- yawancinsu daga kasashen Africa da nahiyar Asia -- sun yi kaura zuwa Afirca ta kudu tun bayan kawo karshen mulkin fararen fata a shekarar 1994.

A kalla mutane 62 ne suka mutu sanadiyar hare-haren da ke da alaka da kin jinin baki a kasar ta Afrika ta kudu tun daga shekarar 2008.