Boko Haram ta kashe mutane 10 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari Kamaru.

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a arewacin Kamaru, lamarin da ya yi sandiyyar mutuwar mutane goma.

Dakarun sojin Kamaru sun ce mayakan kungiyar sun kai harin ne a wani kauye da ke arewacin garin Kolofata, a ranar Alhamis da daddare.

Maharan sun tsallaka kan iyaka zuwa cikin Najeriya, kafin sojojin Kamaru su iso.

Kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a arewacin Kamaru da Chadi da kuma Nijar, amma mafi yawancin hare-harenta a Najeriya ne.