Wata sabuwar cuta ta kashe mutane 14 a Ondo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu na zargin cutar nan ta Ebola ce ta rikide zuwa wata siffar.

A Najeriya, wata cuta da hukumomin jihar Ondo ke cewa ba a san ko wacce iri ba ce, ta hallaka mutane a kalla 14 a jihar.

Cutar ta fito daga karamar hukumar Oda Ire ile, inda rahotanni ke cewa jami'an kiwon lafiya na ciki da wajen kasar na ta fafatikar gano musabbabin wannan cutar domin gudun yaduwar ta cikin al'umma.

Cutar -- wacce ba a gane ko wace nau'i ce ba -- ta sa mutanen Ondo cikin dimuwa saboda bayanan likitocin sun nuna cewa tana kisa cikin kankanen lokaci.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Ondo, Mr. Kayode Akinbade, ya ce kawo yanzu suna kokarin tabbatar da cewa cutar ba ta yadu a tsakanin al'umma ba.

Ya kara da cewa suna aiki da tawagar kwararru domin dakile cutar.

Alamun cutar su ne: ciwon kai mai tsanani da daukewar numfashi, da sanya rashin gani da halaka wanda ya harbu da ita cikin sa'o'i 24.

Wasu dai na zargin cutar nan ce ta Ebola ta rikide zuwa wata cuta.