Kyamar baki: 'Yan sanda sun tarwatsa 'yan cirani

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin basaraken gargajia na Zulu, Zulu Goodswill Zwelethini da rura wutar rikicin.

'Yan sandan Afrika ta kudu sun yi harbi da harsashen roba da kuma gurneti domin tarwatsa 'yan cirani da ke dauke da adduna a birnin Johanesburg.

'Yan ciranin sun ce dole suka dauki makamai domin basa samun kariya kamar yadda ya kamata a yayin da ake ta kai hare-haren kin jinin baki.

An kama mutane 12 bayan hare-haren a kan shagunan baki a birnin Johanesburg a cikin dare, duk da cewa an dauki tsauraran matakan tsaro.

An kashe a kalla mutane biyar sakamakon furucin shugaban gargajiya Zulu Goodwill Zwelethini, yayi na cewa baki su bar kasar Afrika ta Kudu.