An yi amfani da sinadari mai guba a Syria — MDD

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana amfani da iskar gas mai guba a Syria

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ga wani hoton bidiyo wanda ke nuna yadda kananan yara suka mutu sakamakon sanya musu sinadarin iskar gas mai guba samfirin kulorin da ake zargin gwamnatin Syria da yi a watan da ya gabata.

A cikin hoton bidiyon anga kananan yara guda uku 'yan kasa da shekaru hudu suna mutuwa duk da irin kokarin da likitoci suka yi na ceton ransu.

Wani likita dan kasar Syria wanda ya ba wa wadanda aka yi amfani da iskar gas din a kansu agajin gaggawa wanda kuma ya gana da kwamitin sulhun na majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa mutuwar yaran uku kadan ne daga irin misalan amfani da iskar gas din.

Wakiliyar kasar Amurka a kwamitin, Samantha Power, cikin halin damuwa ta ce wannan wani abu ne da ba kasafai ake ganin shi ba kuma mai taba zuciya.