Ana nema wa kasar Yemen agaji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki Moon.

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri na nema wa kasar Yemen agajin gaggawa a yayin da yaki da hare-haren jiragen sama suka tsananta a kasar.

Kwamitin bayar da agajin gaggawa na Majalisar yana son samar da dala miliyan 270 cikin watanni uku domin taimakawa wajen ba da abubuwan more rayuwa cikin gaggawa ga 'yan kasar.

Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce mutane a kalla 150,000 ne suka rasa muhallinsu.

Tashe- tashen hankula a Yemen sun yi kamari ne tunda mayakan Houthi suka cire shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi daga kan mulki a farkon wannan shekarar.