Archbishop Welby na ziyara a Masar

Hakkin mallakar hoto xxx
Image caption Archibishop Justin Welby

A yau Lahadi ne Archbishop na Canterbury ke ziyarar shugabannin addini da na siyasa a Masar domin tattauna karuwar hare haren da ake kaiwa Kiristoci a gabas ta tsakiya.

Archibishop Justin Welby wanda shi ne shugaban darikar Anglican ta duniya, zai kuma yi ta'aziyyar kiristoci Coptic 21 da mayakan IS suka fiffilewa kawuna a Libya.

Limamin yana fatan samun karin bayani daga bakin shugaba Al-Sisi game da hadarin da Kiristoci ke fuskanta.

A lokacin ziyarar ta sa, Archbishop Welby zai ziyarci cibiyar raya addinin musulunci ta Al'Ahzar, domin neman hanyoyin magance barazanar da ake fuskanta.