Ana tsammanin yan cirani da dama sun rasu

'Yan cirani Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan cirani

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce idan aka tabbatar da wadaddan alkaluma to zai kasance hasarar rayuka mafi girma a yunkurin yan cirani na ketarawa zuwa nahiyar turai.

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya ce kawo yanzu an sami gawarwakin mutane 28.

Rahotanni sun ce hadarin ya faru ne yayin da mutanen wadanda suke makare a kwale kwalen kamun kifi suka karkata gefe daya na kwale kwalen suna kokarin darewa wani babban jirgin fasinja da ya doso.

Kasar Italiya na jagorantar gagarumin aikin ceto wanda ya hada da jiragen ruwa a shirin da kuma jiragen sama.