China na son kara tasiri a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban China Xi Jinping ya soma wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Pakistan a yau.

Mr Xi zai kaddamar da wani shirin zuba jari na 'yan kasarsa da zai ci kusan dala biliyan 50, wanda Pakistan take fatan zai kawo karshen rikicin makamashinta, sannan ya sauya kasar zuwa wata cibiyar tattalin arziki a yankin.

Shiri ne da ya kunshi gina wasu tituna da hanyar jirgin kasa da bututai masu tsawon kilomita 3,000, da zasu taso daga tashar jiragen ruwa ta Gwadar a Pakistan zuwa yammacin birnin Kashgar na China

Masu aiko da rahotanniu sunce burin Beijing shine na bunkasa karfin da China take da shi ta fuskar tattalin arziki a tsakiya da kuma kudancin Asiya, da kuma ragewa Kasashen Amurka da Indiya karfi