Hukuncin kisa kan 'yan Muslim Brotherhood

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kungiyar Muslim Brotherhood a lokacin zaman shari'a

Wata Kotu a Masar ta yanke wa 'yan kungiyar Muslim Brotherhood su 22 hukuncin kisa bisa zargin kai hari a kan caji ofis na 'yan sanda.

Ana zarginsu da kai harin ne bayan an hambarar da gwamnatin shugaba Muhammed Morsi a shekara ta 2013

Mutanen su 22, an same su da laifin kashe wani dan sanda a lokacin harin.

Daruruwan 'yan kungiyar Muslim Brotherhood ne aka yanke wa hukuncin kisa, ko daurin shekaru masu yawa a gidan yari, tun lokacin da Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya dare kan mulki.

Gwamnatin Masar ta haramta kungiyar Muslim Brotherhood ta shugaba Muhammed Morsi.